Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta kama wasu ’yan ƙasar China 14 da ɗan Najeriya guda ɗaya a masana’antun sarrafa lithium huɗu da ake zargin suna aiki ba bisa ƙa’ida ba a yankin Ogere na Jihar Ogun.
Sanarwar ta ce jami’an hukumar na shiyyar Legas ta biyu sun kama waɗanda ake zargin ranar Juma’a, 23 ga Oktoba, 2026, bayan samun bayanan sirri da gudanar da sa ido.
- Faransa ta tabbatar da mutum na farko da ya kamu da cutar Shamonda da ake samu a dabbobi
- Sojoji sun bayyana dalilin arangamarsu da ’yan sanda a Filato
A yayin kamen, jami’an sun ƙwato buhunan duwatsun lithium, wayoyin hannu guda 18, kwamfutocin tafi-da-gidanka guda huɗu, na’urorin decoder guda biyu, na’urar sarrafa talabijin da kuma babbar motar dakon kaya.
EFCC ta ce za ta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike kan lamarin.
Hukumar ba ta bayyana sunayen waɗanda aka kama ba, yayin da ake ci gaba da bincike kan zargin gudanar da masana’antun sarrafa lithium ba bisa ƙa’ida ba.