Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce a halin yanzu babu mai cutar Ebola a Najeriya, bayan fitar da mara lafiyar da mijinta zuwa Switzerland domin ci gaba da kula da lafiyarta.

Daraktan WHO na Afirka, Dr. Mohamed Janabi, ya bayyana cewa an fitar da su ne da safiyar Litinin, inda ya ce dukkansu ’yan ƙasar Switzerland ne.

Ya kuma ce lafiyar matar ta inganta bayan ma’aikatan lafiya a Najeriya sun kula da ita.

Janabi ya ce Najeriya za ta ci gaba da sa ido kan mutane 52 da suka yi hulɗa da mara lafiyar, yayin da Switzerland za ta kula da matar da kuma sa ido kan mijinta, wanda shi ma aka saka shi cikin jerin waɗanda suka yi hulɗa da ita.

Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Farfesa Muhammad Pate, ya tabbatar da fitar da matar, yana mai cewa shi ne ya amince da matakin.

Sai dai jami’an WHO sun yi gargaɗin cewa fitar mara lafiyar daga Najeriya ba ta nufin an kawar da dukkan haɗarin yaɗuwar cutar ba.

Najeriya ta tabbatar da bullar cutar Ebola ta nau’in Bundibugyo a ranar 20 ga Oktoba, bayan wata mata da ta dawo daga Uganda ta kamu da cutar.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *