Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta nuna alamar tambaya kan yadda za a danganta ta da kalaman da ke kira ga tashin hankali tsakanin ’yan Najeriya, alhali ta ce ta daɗe tana ƙoƙarin haɗa kan al’umma.
Ƙungiyar ta bayyana cewa ta zuba jari da ƙoƙari wajen gina kyakkyawar dangantaka tsakanin mabiya addinai da ƙabilu daban-daban a faɗin ƙasar.
Ta ce tun kafuwarta kusan shekaru 48 da suka gabata, ta mayar da hankali kan yaɗa ingantattun koyarwar Musulunci da Sunnah ta Annabi Muhammad (SAW).
- NYSC za ta ƙarfafa matakan kare lafiyar ma’aikata da ’yan bautar ƙasa
- Shugaba Tinubu ya taya Lula murna, ya nemi faɗaɗa haɗin gwiwar Najeriya da Brazil
JIBWIS ta ƙara da cewa ayyukanta sun haɗa da gyaran ɗabi’u, bunƙasa ilimi da gudanar da ayyukan agaji domin taimaka wa al’umma.
Ƙungiyar ta jaddada cewa tana goyon bayan zaman lafiya da zaman tare tsakanin mutane, ba tare da la’akari da addininsu, ƙabilarsu ko yankin da suka fito ba.
Ta kuma nuna cewa irin waɗannan manufofi da ayyuka sun kasance ginshiƙan tarihinta, tana mai tambayar yadda za a danganta ta da kalaman da ke ƙarfafa tashin hankali kan ’yan Najeriya.