Rundunar sojin Najeriya ta Operation Hadin Kai ta ce ta kashe mayakan kungiyar ISWAP 16 tare da lalata maboyarsu a hare-haren sama da na manyan makamai da ta kai wasu wurare uku a yankin Tunbunma, kudancin Tafkin Chadi, a jihar Borno.

Sanarwar da Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar a Maiduguri ranar 26 ga Oktoba, ta ce an kai hare-haren ne tsakanin ƙarfe 1:00 zuwa 2:00 na dare, bayan samun bayanan sirri kan kasancewar wasu shugabanni da mayakan ƙungiyar a wuraren.

A cewar rundunar, an kashe mayakan 16 a wuraren da aka kai wa hari, daga cikin waɗanda aka ce sun mutu akwai Abu Zubiru, wanda rundunar ta bayyana a matsayin ɗan ƙasar Larabawa ne, da wasu mutum biyu masu suna Baana Nglewa da Jindullah Sadiq, tare da wasu mayaka.

Sanarwar ta kuma ce Abu Saleem, wanda rundunar ta bayyana a matsayin Wali na Tunbunma, ya samu munanan raunuka, tare da wasu mutum bakwai, sai dai sanarwar ba ta yi cikakken bayani kan irin raunin da suka samu ko halin da suke ciki ba.

Rundunar ta ce za ta ci gaba da kai hare-haren domin dakile ayyukan ƙungiyoyin ta’addanci da hana su samun mafaka a yankin Arewa maso Gabas.

Wannan na zuwa ne bayan wasu hare-haren da Operation Hadin Kai ta ce ta kai kan wuraren ISWAP a baya-bayan nan.

Sojojin sun kuma buƙaci jama’a da su riƙa kai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai cikin gaggawa domin taimakawa ayyukan yaƙi da ta’addanci da dawo da zaman lafiya a yankin.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *