Jihar Yobe tace ana zargin  mutane 511 ne suka kamu da cutar mashako, yayin da  13 kuma suka rigamu gidan gaskiya.

Kwamishinan Lafiya da Ayyukan Jin Ƙai na Jihar, Muhammad Gana, shi ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) a Damaturu.

Mista Gana ya yi bayanin cewa mutane 13 da suka mutu suna wakiltar kashi 2.5 cikin ɗari na waɗanda suka kamu da cutar, wanda ya fi ƙasa da adadin da ake samu a yawancin sauran jihohin da cutar ta shafa a faɗin ƙasar.

Ya tabbatar da cewa ɓullar cutar ta shafi ƙananan hukumomi 12 a jihar, kuma shirye-shiryen yi wa jama’a riga-kafi a waɗannan yankuna suna tafiya yadda ya kamata.

Mista Gana ya ƙara da cewa jimillar mutane 511 da suka kamu da cutar a yanzu ya ragu sosai idan aka kwanta da mutane 1,100 da aka tabbatar a watan Satumban shekarar 2025 da kuma shekarun baya.

Ya ce hakan ta faru ne  tun daga shekarar 2023—lokacin da jihar ta sami mafi yawan adadi na mutane 3,080 da suka kamu—a kan matakan gaggawa da kuma ayyukan magance cutar da ake ci gaba da gudanarwa.

Ayyukan da Kwamishinan ya lissafa sun haɗa da ba da magunguna kyauta ga waɗanda cutar ta shafa da horar da ma’aikatan lafiya kan dabarun karɓar lamarin da gudanar da riga-kafi na musamman a yankunan da ke da wuyar isa da sa hannun al’umma da kuma gangamin wayar da kai kan cutar.

Sauran ƙoƙarin sun haɗa da binciken waɗanda suka yi mu’amala da masu cutar cikin tsauri ta hannun ma’aikatan lafiya da rarraba sabbin bayanai ga masu ruwa da tsaki da yin tarukan haɗin gwiwa akai-akai, da kuma tara albarkatu domin murƙushe ɓullar cutar.

Mista Gana ya yaba wa goyon bayan da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Hukumar Agajin Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), da kuma Ƙungiyar AFENET (African Field Epidemiology Network) suka bayar wajen taimakawa gangamin yi wa jama’a riga-kafi a jihar, musamman a tsakanin makiyaya.

Mashako wata cuta ce ta ƙwayar cuta (bakteriya) wadda galibi take shafar maƙogwaro da hanyoyin numfashi.

Galibi tana yaɗuwa ne ta hanyar ruwan numfashi da ake feshawa yayin tari ko atishawa, wani lokacin kuma ta hanyar mu’amala ta kai tsaye da ciwon fata na wanda ke ɗauke da cutar ko ruwan da ya fito daga jikinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *