Wani matashi da ba a kaiga tantance ko waye ba ya farmaki wani malamin addinin Musulunci, Malam Musa Lukwa, a jihar Sokoto jim kaɗan bayan ya jagoranci sallar Juma’a a masallacinsa da ke yankin Mabera na birnin.

Rahotanni sun ce matashin, wanda  ya shiga cikin masu ibada ya kai wa malamin hari, inda ya daba masa wuƙa sau biyu a wuya.

Majiyoyi sun bayyana cewa wanda ake zargin yana zaune ne cikin masu ibada, a ɗaya daga cikin layukan gaba, kafin ya kai wa malamin harin nan take bayan an idar da sallar.

Majiyoyin sun ƙara da cewa masu ibadar sun yi nasarar cafke wanda ake zargin, inda suka lakada masa duka har ya mutu.

Rahotanni sun danganta harin da wani wa’azi da malamin ya gabatar a baya, inda ya kawo wani Hadisi da wasu malaman addinin Musulunci, musamman masu alaƙa da Ɗariƙa, suka ɗauka a matsayin abin da ya ɓatawa iyayen Annabi Muhammad rai.

Bayan wannan ce-ce-ku-ce, matashin da aka bayyana da suna Mai Barewa, ya yi barazanar kashe Malam Musa Lukwa da babban ɗalibinsa, Malam Murtala Assada.

Daga bisani, malamin da mabiyansa sun kai rahoton barazanar ga ‘yan sanda, lamarin da ya kai ga kama wanda ake zargin tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

Kotun ta bayar da umarnin tsare shi a gidan gyaran hali na wani lokaci, yayin da shari’ar ta ci gaba da kasancewa a gabanta.

Kwanaki huɗu kafin faruwar lamarin na ranar Juma’a, malaman sun kuma ziyarci gidan gwamnatin jihar Sokoto, inda suka gabatar da rubutaccen ƙorafi game da batun.

Da yake tabbatar da harin, Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce Malam Lukwa na karɓar magani a Asibitin Kwararru na Sokoto.

Ya ce mutumin da ake zargin ya kai harin an kashe shi ne nan take.

Rufa’i ya ce kawo yanzu ba a kama wani mutum dangane da tashin hankalin da ya biyo bayan lamarin ba, yana mai cewa rundunar ta ɗauki matakan da suka dace domin hana al’amuran ƙara ta’azzara.

Ya ce rundunar na gudanar da bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa harin tare da gano duk wani mutum da ka iya kasancewa cikin lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *