Gwamnatin Tarayya ta sanar cewa daga ranar 1 ga Oktoba, 2026, ɗaliban Najeriya za su fara samun megabytes 100 na data kyauta a kowace rana domin gudanar da bincike a shafukan ilimi da aka amince da su guda na dijital.
Wannan shiri, wanda Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ke aiwatarwa tare da haɗin gwiwar kamfanonin sadarwa da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, zai fara ne da ɗaliban makarantun sakandare na gwamnati (Senior Secondary) da na manyan makarantun gaba da sakandare.
Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, ya bayyana ranar da za a fara shirin a ranar Alhamis yayin ƙaddamar da Shiri na Samar da Data Kyauta Domin Samun Damar Amfani da Shafuka da Abubuwan Ilimi a Najeriya, wanda aka yi a Abuja.
“Za a samar da wannan damar ga ɗaliban Najeriya daga ranar 1 ga Oktoba, 2026,” in ji Alausa, yayin da yake godiya ga gudunmawar da Ƙungiyar Masu Lasisin Kamfanonin Sadarwa ta Najeriya (ALTON) ta bayar ga shirin.
-
Wacce rawa Ƙasar Jordan ke takawa a rikicin Gabas ta Tsakiya
-
FRSC ta ƙaddamar da yunƙurin kawo ƙarshen lodin wuce kima
-
Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta kama mutum biyu bisa zargin kisa
A ƙarƙashin wannan tsari, kamfanonin sadarwar tarho da ke sa hannu za su riƙa bayar da kyautar data ta MB 100 a kullum, wanda masu cin gajiyar za su iya amfani da ita kawai a shafukan yanar gizo da manhajojin ilimi da aka amince da su.
Da yake ƙarin bayani, Alausa ya ce shirin zai fara ne da ɗaliban makarantar sakandare na gaba da kuma na manyan makarantu, kafin daga bisani a faɗaɗa shi zuwa sauran ɗalibai.
“Burinmu shi ne, a ƙarshe, kada wani ɗalibin Najeriya ya rasa samun damar yin amfani da ingantattun abubuwan ilimi kawai saboda ba ya da ƙarfin siyan data,” in ji ministan.
Ya lura cewa tsadar datan yanar gizo ta zama babbar tarnaƙi ga ilimin dijital, musamman ga yaran da suka fito daga iyaye marasa ƙarfi.
A cewarsa, samar da damar yin amfani da shafukan ilimi ba tare da biyan kuɗin data ba zai iya mai da wayoyin hannu, kwamfutoci masu taɓawa (tablets) da sauran kwamfutoci su koma ajujuwan karatu da ɗakunan karatu na littattafai ga ɗaliban da da za su sha wahala wajen samun abubuwan ilimi na dijital.
Haka zalika, ministan ya bayyana cewa gwamnati tana duba matakan da za su takaita amfani da yanar gizo ga yaran da shekarunsu suka gaza 16, inda ake saftataccen tsammanin sanar da ƙarin bayani a nan gaba.
Ya ce dole ne abubuwan ilimin da ake samar wa yara su kasance “masu dacewa, ingantattu, amintattu kuma sun yi daidai da manufofin iliminmu da tsarin karatunmu.”
Alausa ya ƙara da cewa, “Za a ƙayyade amfani da yanar gizo ga yaran da ba su kai shekara 16 ba,” inda ya ce za a fitar da sanarwa ta gaba kan matakin da aka tsara.
Ministan ya kuma ce gwamnati tana faɗaɗa tsarin yin amfani da fasahar dijital a ɓangaren ilimi ta hanyar Tsarin Bayanan Ilimi na Najeriya (NEDI), Tsarin Gudanar da Bayanan Ilimi na Dijital na Najeriya (NDEMIS), da Lamba Shaida ta Ɗalibi (LIN).
Ya bayyana cewa fiye da makarantu 240,000 aka riga aka yi wa taswirar wuraren da suke a faɗin ƙasar, yayin da gwamnati ke maida Binciken Shekara-shekara na Makarantu zuwa na dijital domin samun ingantattun bayarai kan yawan ɗalibai, malamai, ajujuwan karatu, ɗakunan gwaje-gwaje, ɗakunan karatu, haɗin yanar gizo da kuma tsaron makarantu.