Amnesty International ta yi tir da allawadai mai karfi kan harin da ‘yan sanda dauke da makamai suka kai ta hanyar da ta sabawa doka a gidan talabijin da rediyo na JKD (JKD TV Hamada Radio Network) da ke Millennium City a Kaduna.

An kama Babban Manaja Charles Abah tare da wani ma’ikaci ba tare da bin ka’ida ba yayin samamen.

‘Yan sanda sun bayyana cewa sun sami umarnin kame yar jarida Zainab Salihu Yabagi ne sakamakon wani bidiyon bayani da JKD Radio & Television ta samar game da Mista Ibrahim Kabir Masari, Mai Shawara na Musamman ga Shugaban Kasa kan Al’amuran Siyasa.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta riga ta sanar da neman Zainab Yabagi ruwa a jallo.

Gwamnatin Najeriya na kara tsaurara wa kafafen labarai damar gudanar da rahotanni kan abubuwan da suka shafi bukatun jama’a ba tare da tsoron farmaki ko sakayya ba.

Hari kan gidan rediyo da talabijin na JKD yana daya daga cikin matakan da ake dauka na haifar da yanayin tsoro a tsakanin kafafen labarai a Najeriya da kuma karkarfe aikin ‘yan jarida.

Nufar kafafen labarai masu zaman kansu na da manufar tauye wa jama’a damar samun adalcin rahotanni da ba son kai kan al’amuran da suka shafi rayuwarsu.

Babu wani jami’in gwamnati — ko da wane irin matsayi yake da shi — da ya wuce bincike ko kushe domin bukatun jama’a.

Hari kan kafafen watsa labarai hari ne kan ‘yanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *