Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun amince da wata yarjejeniyar haɗin gwiwa ta ƙungiyar BRICS da ta yi kira da a nuna kamun kai a yaƙin da ake yi a Gabas ta Tsakiya a ranar Asabar, lamarin da ake gani a matsayin wata alama ta samun ci gaba a fannin diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu da yaƙin ya raba.
Ofishin yaɗa labarai na Abu Dhabi ya bayyana a shafinsa na X cewa shugabannin ƙasashen biyu sun tattauna batutuwan yankin da na ƙasa da ƙasa, da hanyoyin rage tashin hankali, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da kuma ƙoƙarin inganta zaman lafiya da ci gaban yankin. Sai dai ofishin bai bayyana ko an cimma wata matsaya a tattaunawar ba.
- Ku samar da kuɗaɗe don kare halittu – BRICS ga G7
- Ƙasashen BRICS zasu haɗa gwiwa a fannin lafiya da yakar cutar tarin fuka
- BRICS ta ce Bankin NDB zai taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasashe masu tasowa
Ana Kallon Taron ƙoli na BRICS a matsayin gwaji ga ƙarfin diflomasiyyar ƙungiyar da aka kafa a shekarar 2009 domin kalubalantar tsarin duniya da Amurka da kawayenta na Yamma suka fi rinjaye.
Asalin ƙungiyar ta ƙunshi Brazil da Rasha da Indiya da China da Afirka ta Kudu, kafin daga bisani ta faɗaɗa tare da ƙara Masar, Habasha da Indonesia, da kuma Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa.
A yayin rikicin, Iran ta kai hare-hare da dama kan Hadaddiyar Daular Larabawa, wanda na baya-bayan nan ya faru a ƙarshen watan Agusta, lokacin da ta kai hari kan sansanin sojin sama na Al Minhad, wanda ke ɗauke da sojojin Amurka da jirage masu saukar ungulu.