Shugabannin ƙasashen BRICS sun yi kira a ranar Asabar da a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin lafiya, ciki har da musayar ƙwarewa da sabbin dabaru da kuma ingantattun hanyoyin aiki.

Sun kuma amince da wasu shirye-shirye da suka shafi yaƙi da cutar tarin fuka, kiwon lafiya ta hanyar fasahar zamani da samar da rayuwa mai ƙoshin lafiya da kula da lafiyar ƙwaƙwalwa da kuma magungunan gargajiya.

A cikin yearjejeniyar New Delhi, shugabannin sun ce sun sake tabbatar da aniyarsu ta inganta samar da kiwon lafiya ga kowa ta hanyar amfani da “tsare-tsare masu ƙarko, da kuma mayar da hankali kan jama’a.”

Shugabannin sun kuma sake jaddada “imaninsu na bai ɗaya cewa dole ne a kiyaye tare da ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashe da dama a fannin lafiya”, tare da jaddada muhimmiyar rawar da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ke takawa wajen daidaita harkokin kiwon lafiya a duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *