Ƙungiyar BRICS bayyana matuƙar damuwa kan ƙarin harajin kwastam na bai ɗaya da wasu matakan da ba na haraji ba, waɗanda ke kawo cikas ga harkokin kasuwanci tare da saba wa ƙa’idojin Ƙungiyar Ciniki ta Duniya (WTO).
Haka kuma, BRICS ta yi Allah-wadai da sanya wasu matakan tilasci na bai ɗaya waɗanda suka saba wa dokokin ƙasa da ƙasa, tare da ƙarfafa ci gaba da tattaunawa domin samar da hanyoyin da suka dace wajen biyan kuɗaɗen cinikayya tsakanin ƙasashen BRICS.
Firaministan Indiya, Narendra Modi, ne ya gabatar da shawarar amincewa da daftarin yarjejeniyar a hukumance yayin taron shugabannin ƙungiyar.
- ƙungiyar BRICS ta amince da yarjejeniyar New Delhi
- Taron Kungiyar BRICS: Abubuwan da za a tattauna da muhimmancin su
- Trump ya zargi Iran da kai hari kan bututun mai na Saudi Arabiya
Yarjejeniyar BRICS ta sanya harkokin kasuwanci a matsayin muhimmin ginshiƙi a cikin ajandar tattalin arziƙin ƙungiyar, inda ƙasashe mambobin ƙungiyar suka bayyana matuƙar damuwa kan ƙarin harajin kasuwanci na bai ɗaya da wasu matakan da ba na haraji ba, waɗanda ke kawo cikas ga kasuwanci tare da saba wa ƙa’idojin Ƙungiyar Ciniki ta Duniya (WTO).
Haka kuma, ƙungiyar ta yi Allah-wadai da matakan tilastawa na bai ɗaya waɗanda suka saba wa dokokin ƙasa da ƙasa.
Wannan matsayi ya kasance batu da ake yawan tattaunawa a cikin BRICS, yayin da ƙasashe mambobin ƙungiyar ke ƙoƙarin rage dogaro da tattalin arziƙinsu ga matsin lamba na tattalin arziƙi daga ƙasashen waje.