Shugabannin ƙungiyar BRICS ta ƙasashe masu tasowa ta amince da wata yarjejeniya da aka kira da ‘New Delhi declaration’ a ranar Asabar, inda suka bayyana matuƙar damuwa kan ƙarin harajin kwastam da wasu matakan da ƙasashe ke ɗauka na bai ɗaya, waɗanda suke kawo cikas ga kasuwanci tare da saba wa ƙa’idojin Ƙungiyar Ciniki ta Duniya (WTO).
Ƙungiyar, wadda yanzu ta ƙunshi ƙarin ƙasashe, ta kuma nuna ƙoƙarin haɗin kai kan batutuwan kasuwanci da siyasar duniya da yadda ya kamata a tafiyar da harkokin mulkin duniya.
BRICS ta kuma yi Allah-wadai da sanya wasu matakan tilastawa na bai ɗaya, waɗanda suka saba wa dokokin ƙasa da ƙasa, tare da ƙarfafa ci gaba da tattaunawa domin samar da hanyoyin da suka dace wajen sauƙaƙa biyan kuɗaɗen cinikayya tsakanin ƙasashen BRICS.
- Taron Kungiyar BRICS: Abubuwan da za a tattauna da muhimmancin su
- Trump ya zargi Iran da kai hari kan bututun mai na Saudi Arabiya
- Bore yayi ajalin mutane 7 a wani gidan yari a arewacin Siriya
Firaministan Indiya, Narendra Modi, ne ya gabatar da shawarar amincewa da sanarwar a hukumance yayin taron shugabannin ƙungiyar.
‘Yarjejeniyar New Delhi ta shekarar 2026 tana gabanmu. Ta ƙunshi ainihin abubuwan tattaunawarmu, tare da bayyana ra’ayoyinmu kan muhimman batutuwan duniya da na yankuna. Haka kuma, ta fayyace abubuwan da za mu fi mayar da hankali a kansu domin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar BRICS. Idan babu wata ƙasa da ke da ƙorafi, ina ba da shawarar mu amince da yarjejeniyar’.
Modi ya ce sanarwar ta ƙunshi muhimman abubuwan da aka tattauna a taron, tare da bayyana ra’ayoyin ƙasashen BRICS kan manyan batutuwan duniya da na yankuna, da kuma abubuwan da ya kamata a mayar da hankali a kansu domin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar ƙungiyar.
Ya ce: “yarjejeniyar New Delhi ta shekarar 2026 tana gabanmu. Ta ƙunshi ainihin abubuwan tattaunawarmu, tare da bayyana ra’ayoyinmu kan muhimman batutuwan duniya da na yankuna. Haka kuma, ta fayyace abubuwan da za mu fi mayar da hankali a kansu domin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar BRICS. Idan babu wata ƙasa da ke da ƙorafi, ina ba da shawarar mu amince da sanarwar.”
Bayan da babu wata ƙasa da ta nuna adawa, shugabannin BRICS sun amince da Sanarwar New Delhi ta 2026 baki ɗaya.
Amincewar ta kasance wani gagarumin ci gaba na diflomasiyya ga ƙungiyar, musamman bayan da taron ministocin harkokin wajen BRICS da aka gudanar a New Delhi a watan Mayu ya kasa fitar da sanarwar haɗin gwiwa sakamakon rashin jituwa tsakanin Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da Amurka da Iran suka koma musayar hare-hare bayan dakatar da faɗa da aka yi a mafi yawan watan Agusta, a cikin yaƙin da ya shafe watanni shida.
Haka kuma, ‘yan tawayen Houthi masu alaƙa da Iran a Yemen sun ƙara ƙarfafa matsayinsu a yankin Bahar Maliya.