Daga Ibrahima Yakubu
Mata da ƴan mata guda 45—waɗanda suka haɗa da Musulmi da Kiristoci masu shekaru tsakanin 16 zuwa 55—suka samu horo a fannin gina zaman lafiya da shiga tsakani wajen warware ɗauki-ba-daɗi, da kuma yin tattaunawa tsakanin al’umma a garin Kasuwan Magani na ƙaramar hukumar Kajuru a Jihar Kaduna.
Ƙungiyar Mata ta Addinai Daban-daban (Interfaith Women Kasuwan Magani) ce ta shirya wannan horo na yini ɗaya, tare da goyon bayan Cibiyar Shiga Tsakani ta Addinai (IMC) da ke Kaduna.
Wannan yana ɗaya daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa rawar da mata ke takawa wajen rigakafin tashe-tashen hankula da kuma haɓaka zaman lafiya a al’ummomin da rikice-rikicen cikin gida suka shafa.
Yayin da yake jawabi a gurin taron, Mista Jonathan Peter, wanda shi ne ya tsara shirin, ya bayyana cewa an shirya horon ne domin faɗakar da mata ingantattun hanyoyin ciyar da zaman lafiya gaba da warware sabani, da kuma ƙarfafa tattaunawa a tsakanin al’umma.
Ya yi bayanin cewa mata suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen gano ɓangarorin da ke tasowa tun daga tushe, da kuma hana rikici rikide wa zuwa tashe-tashen hankula.
- BRICS ta ce Bankin NDB zai taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasashe masu tasowa
- Dakatar da yaki: Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun goyi bayan BRICS
- Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Bamanga Tukur, ya rasu.
Wannan shiri an keɓance shi ne musamman domin mai da martani ga tarihin garin Kasuwar Magani na fuskantar rikicin addini ko na al’umma, gami da matsin lamba kan hanyoyin samun abincin yau da kullum da albarkatun ƙasa sakamakon sauyin yanayi.
Har ila yau, horon ya haɗa mata da ƴan mata, ciki har da zawarawa da matasa, da kuma waɗanda suka tsira daga tashe-tashen hankula, da nufin taimaka musu wajen sauyawa daga kasancewa waɗanda rikici ke ɗauka zuwa masu kera zaman lafiya da kuma zama na farko wajen ba da ɗauki a cikin al’ummarsu.
Horon ya ƙunshi fannoni daban-daban da suka haɗa da Hanyoyin Warware Rikici ba tare da Kotu ba (ADR) da dabarun shiga tsakani da haƙƙoƙin mata da ƴan mata da rigakafin cin zarafi daban-daban dake tsakanin maza da mata (GBV) tare da tallafa wa waɗanda aka yi wa, tsarin ba da samamen gargaɗin farko da amsawa cikin sauri (EWER) gami da dangantakar da ke tsakanin sauyin yanayi, gasar neman albarkatu, da kuma ɓullar rikici.
Masu halarta sun sami damar shiga cikin bita ta hanyar tattaunawa da kwaikwayon yanayi, da kuma gwaje-gwajen aikace-aikace, waɗanda aka tsara domin ƙarfafa ikonsu na mayar da martani ga sabani da barazanar da ke ɓullewa a cikin al’ummominsu.
A cewar masu shirya shirin, binciken da aka gudanar kafin da kuma bayan horon ya nuna samun haɓaka har na ƙashi 85 cikin ɗari a kan ilimin masu halarta da kuma aikace-aikacensu na shiga tsakani yayin gwaje-gwajen warware rikici.
Ɗaya daga cikin babbar nasarar da shirin ya cimma ita ce ƙafa Hukumar Jakadun Zaman Lafiya ta Mata ta Kasuwan Magani a hukumance.
Wannan cibiya ta haɗa mata 45 da suka halarci horon domin su zama runduna a matakin tushe da za su iya ɗaƙile jita-jita su kuma shiga tsakani a rikice-rikice da gano alamomin farko na rikici, da kuma tallafa wa waɗanda aka yi wa cin zarafi ta hanyar tura su wajen da ya dace.
Wata mai halarta ta bayyana cewa shirin ya sauya yadda mata da dama ke kallon matsayinsu wajen rigakafin rikici.
Ta lura cewa matan da a baya suke jiran maza su shiga tsakani a sabanin da ke faruwa a al’umma, yanzu suna jin cewa suna da dukkan dabarun da ake buƙata domin shiga tsakani a maƙwabtaka da kuma ɗaukar matakin wuri kafin tashe-tashen hankula su tsananta.
Masu shirya taron sun ce samar wa mata dabarun gina zaman lafiya zai iya ƙarfafa juriyar al’umma saboda mata ne galibi ke farkon fahimtar tashin hankali a cikin iyali ko maƙwabtaka.
Domin dorewar tasirin wannan shiri, shugabannin aikin sun ba da shawarar gudanar da bincike da kulawa akai-akai ga Jakadun Zaman Lafiya ta Mata da ƙulla ingantacciyar dangantaka da jami’an tsaro da Kwamitin Zaman Lafiya na Ƙaramar Hukumar Kajuru, gami da faɗada irin wannan horo zuwa maƙwabtan al’ummomin da suka shahara wajen rikici.
Masu tsara shirin kuma sun jaddada buƙatar samun haɗin kai mai dorewa a tsakanin shugabannin mata da cibiyoyin addini da sarakunan gargajiyada ƙungiyoyi masu zaman kansu da ma’aikatun gwamnati domin tabbatar da cewa mata sun ci gaba da shiga ta hanyar aiki wajen gina zaman lafiya, ba da gargaɗi a kan lokaci, da kuma tattaunawar al’umma.
Wannan shirin yana nuna yadda zuba jari a fannin jagorancin mata da samar musu da ingantattun dabarun gina zaman lafiya zai iya taimakawa wajen rigakafin tashe-tashen hankula gami da gina al’ummomi masu juriya da samun lafiyar juna a yankunan da rigingimu suka ɗaidaita.