Tarayyar Turai, za ta gabatar da sabuwar doka a ranar Alhamis, da nufin kare yara daga illolin kafafen sada zumunta, kwana guda bayan shugabar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta bayyana shawarar kayyade shekarun da yara za su iya fara amfani da wadannan kafafe.

Matakin ya biyo bayan shafe sama da shekara guda ana tattaunawa kan batun, tare da matsin lamba daga wasu kasashen kungiyar ciki har da Faransa da Girka, da kuma iyaye a fadin kasashe 27 na Tarayyar Turai.

Ana sa ran von der Leyen za ta yi magana kan batun ne a yayin wani jawabi da za ta gabatar a gaban Majalisar Dokokin Tarayyar Turai da ke Strasbourg.

Kakakin Tarayyar Turai, Olof Gill, ya ce za a gabatar da dokar mai suna “EU Kids Act” a ranar Alhamis a birnin Brussels, inda von der Leyen za ta gabatar da ita tare da kwamishiniyar Tarayyar Turai mai kula da harkokin fasaha, Henna Virkkunen.

Har ila yau, von der Leyen na nazarin yiwuwar hana yara ‘yan kasa da shekara 13 amfani da kafafen sada zumunta gaba daya, kamar yadda kwamitin kwararru ya ba da shawara, ko kuma a kayyade shekarun zuwa kasa da 15, wanda Faransa ke goyon baya.

Ostiraliya ce ta zama kasa ta farko a duniya da ta haramta wa ‘yan ƙasa da shekara 16 amfani da kafafen sada zumunta, yayin da gwamnatoci da kwararru ke ƙara nuna damuwa kan mummunan tasirin da amfani da kafafen ke yi ga lafiyar kwakwalwa da ta jiki na yara, kamar yadda bincike da dama ya tabbatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *