Shugaban mulkin sojan Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya gana da wakilin Biritaniya Richard Crowder, domin tattauna hanyoyin kawo ƙarshen yaƙin basasar ƙasar.
Ganawar ta kuma mayar da hankali kan yadda za a rage wahalhalun fararen hula da kuma matsalar kare haƙƙin ɗan Adam da ke ƙara ta’azzara.
Mista Crowder, wanda shine Babban Wakilin Birtaniya na Musamman kan Al’amuran Sudan ya ce Biritaniya, na ba da fifiko wajen kawo ƙarshen rikicin ta hanyar tattaunawar da ’yan Sudan.
Ya jaddada buƙatar samar da tsarin siyasa mai cike da gaskiya wanda zai baiwa ’yan Sudan da ke ciki da wajen ƙasar damar bayyana ra’ayinsu.
An kuma tattauna rahoton kwamitin binciken haƙƙin ɗan Adam na Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda ya bayyana zarge-zargen cin zarafi da dama da kuma tsoma bakin ƙasashen waje game da yakin.
Rahoton ya ce, wasu ƙungiyoyi da ke da alaƙa da Hadaddiyar Daular Larabawa sun taimaka wajen ɗaukar hayar sojojin haya ’yan Colombia domin su yi yaƙi tare da dakarun Rapid Support Forces, wato RSF.
Biritaniya ta gabatar da wani ƙuduri na tsawaita wa’adin aikin kwamitin binciken haƙƙin ɗan Adam na Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda wa’adinsa zai ƙare a watan Oktoba.
Sai dai gwamnatin Sudan, da sojoji ke jagoranta na adawa da matakin, tana cewa hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke kula da haƙƙin ɗan Adam a ƙasar sun wadatar.
Crowder ya ce lalata muhimman ababen more rayuwa da kuma gudun hijirar miliyoyin mutane zuwa ƙasashen makwabta sun ƙara tsananta abin da ya bayyana a matsayin mafi muni cikin rikice-rikicen jin kai a duniya.
Ya ce ana sa ran batun Sudan zai kasance cikin muhimman abubuwan da za a tattauna a taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya mai zuwa a birnin New York.
- Najeriya ta miƙa buƙatar karɓar baƙuncin Gasar Motsa Jiki ta Duniya ta 2030
- Chelsea ta yi wa Manchester United wankin babban bargo da ci 5-0
-
Manchester City ta doke Man United da mutum 10 a Old Trafford
A gefe guda kuma, masu aikin agaji sun yi gargadin cewa yunwa mai tsanani na dab da afkawa wasu yankuna shida a jihar West Kordofan sakamakon fari, lalacewar amfanin gona da tashin farashin abinci.
Ƙungiyar tallafawa fararen hula Dar Hamar Emergency Room, ta ce yankunan da abin ya shafa sun haɗa da Wad Banda da El Nuhud da Ghebeish da Abu Zabad da Al Odaiya da Al Khiwai.
Ta ce hare-hare da zarge-zargen satar dukiyoyin jama’a da ake dangantawa da dakarun RSF sun tilasta dubban fararen hula barin gidajensu zuwa North Kordofan.
Ƙungiyar ta ce harin ya jawo lalacewar gonaki da kuma gazawar amfanin gona gaba ɗaya, yayin da farashin buhun dawa, wanda shi ne babban abincin yankin, ya kai kusan fam miliyan goma na Sudan, kwatankwacin dala 1,300.
Ta ce takunkumin takaita zirga-zirga da RSF ta kakaba, ciki har da hana manyan motocin kasuwanci shigar da kayan abinci daga North Kordofan, ya ƙara dagula matsalar.
Yara da tsofaffi ne suka fi fuskantar yunwa da cututtuka, yayin da aka riga aka samu rahoton mace-mace a wasu yankuna saboda ƙarancin taimakon jin ƙai na ƙasa da ƙasa.