Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, tare da hadin gwiwar sojoji, sun kashe wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne yayin wani samame na hadin gwiwa da suka gudanar a Dajin Gumki da ke Kangiwa, a Karamar Hukumar Arewa ta jihar.

An gudanar da samamen ne da misalin karfe 6:05 na safe ranar Litinin, 14 ga Satumba 2026, inda jami’an tsaron suka kwato bindigogi da alburusai da babura da wasu kayayyaki da ake zargin na ‘yan ta’addan ne.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya fitar, ya ce Dajin Gumki wata sananniyar hanya ce da ‘yan bindiga da mayakan Lakurawa ke amfani da ita wajen gudanar da ayyukansu.

Ya ce jami’an tsaron sun yi artabu da ‘yan ta’addan yayin samamen, inda suka samu nasarar kashe wasu daga cikinsu.

Kayayyakin da aka kwato sun hada da bindiga ƙirar PKT guda daya da harsasai 174, da bindiga ƙikrar AK-47 guda daya da harsasai 14,  sai wayoyin hannu guda biyu, da babura hudu, da kayan soji guda biyu

Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar wa mazauna yankin cewa ayyukan hadin gwiwar jami’an tsaro za su ci gaba har sai an kawar da miyagun laifuka gaba daya daga dajin da kuma hanyoyin da ke makwabtaka da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *