Dakarun Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun kama wani da ake zargin dillalin miyagun kwayoyi ne a Jihar Kaduna, tare da dakile wani harin ‘yan ta’adda da kuma ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su a Jihar Sokoto.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Yada Labarai na Rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar, inda ya ce dakarun sun samu nasarorin ne, yayin wasu samame daban-daban da suka gudanar a ranakun 12 da 13 ga Satumba, 2026.
A cewar Aliyu Danja, a ranar 12 ga Satumba, dakarun Sashi na Farko sun tare wani mutum mai suna Yohana Musa, yayin aikin binciken ababen hawa da suka gudanar a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.
- Tinubu ya bayar da umarnin sakin kudaden da aka ware wa hukumomin raya yankuna
- Gwamnatin Kaduna ta kwato hekta 500,000 na gonakin da ‘yan bindiga suka mamaye
- Tinubu ya isa Paris don ci gaba da hutun shekara a Turai
Ya ce an kama Musa ne dauke da dimbin miyagun kwayoyi da wasu haramtattun abubuwa, a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Birnin Gwari, kuma a yanzu haka yana hannun dakarun domin gudanar da bincike.
A wani samame na daban ranar 13 ga Satumba, dakarun Sashi na Biyu sun mayar da martani kan kiran neman dauki bayan ‘yan ta’adda sun kai hari a Unguwan Lalle da ke Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto.
Aliyu Danja ya ce dakarun sun yi arangama da ‘yan ta’addan tare da bude musu wuta, lamarin da ya tilasta musu ja da baya cikin rudani, yayin da dakarun suka samu nasarar ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su.