Ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike, ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta kammala dukkan ayyukan titunan da ake aiwatarwa a Abuja kafin ƙarshen shekarar 2026.
Wike ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis bayan ya duba ci gaban manyan ayyukan tituna guda biyu, waɗanda suka haɗa da yankin Jami’ar Nile da ke Research and Institution District zuwa Lugbe, da kuma Arterial Road N1 daga Wuye District zuwa Ring Road II.
Ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta himmatu wajen kammala dukkan ayyukan da ta fara, yana mai jaddada cewa ba za a bar wani aikin hanya a baya ba.
Ministan ya ce yana da cikakken kwarin gwiwa cewa dukkan ayyukan da aka ƙaddamar a ƙarƙashin wannan gwamnati za su kasance a kammale kafin ƙarshen shekara.
Da yake magana kan aikin Research and Institution Avenue da kamfanin China Civil Engineering Construction Corporation (CCECC) ke gudanarwa, Wike ya ce da farko ya nuna damuwa kan irin aikin da ya rage, amma bayan duba ci gaban da aka samu ya gamsu cewa za a kammala aikin a kan lokaci.
”Ya ce na yi imani gwamnati zata cika alƙawarin da ta dauka akan ayyukan titunan, daga abin da na gani a yau, ina da yakinin cewa za a kammala wannan aikin. Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta samar da muhimman ababen more rayuwa da ke sauya fasalin Abuja,” in ji shi.
- Tinubu ya rusa Kwamitin sa ido kan sayar da kadarorin gwamnati
-
Tinubu ga Gwamnoni: Ku daina gina gadoji inda ba a buƙatar su
Wike ya kuma yabawa kamfanin Arab Contractors kan yadda yake gudanar da wani muhimmin aikin hanya a babban birnin tarayya.
Ya tunatar da cewa lokacin da gwamnati ta karɓi ragamar mulki a watan Agustan 2023, aikin hanyar Airport Road zuwa Kuje bai fara ba. Sai dai bayan tattaunawa da gwamnati, kamfanin ya ɗauki alƙawarin kammala aikin cikin lokacin da aka tsara.
Ministan ya ce kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Hukumar FCTA da kamfanonin kwangila ce ta sa ake samun ci gaba cikin sauri.
A cewarsa, wasu kamfanoni kan ci gaba da aiki ko da ba a kammala biyan su kuɗaɗen kwangila ba, saboda suna da tabbacin cewa gwamnati za ta cika dukkan alƙawuran da ta ɗauka.
Ya bayyana jin daɗinsa da irin ci gaban da ake samu yana mai cewa sauye-sauyen da ake gani sun tabbatar da ƙoƙarin gwamnatin Tinubu wajen inganta manyan ababen more rayuwa.
Ya kuma buƙaci kafafen yaɗa labarai su ci gaba da ba da rahotanni cikin gaskiya da adalci game da ayyukan ci gaban da ake gudanarwa a babban birnin tarayya.
Dangane da aikin gadar Jabi, Wike ya buƙaci jama’a su ƙara haƙuri, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin Abuja za ta kammala dukkan ayyukan da ta fara kafin ƙarshen shekarar 2026.