Hukumomin tsaro a ƙasar Liberia sun ƙona hodar iblis mai nauyin kusan tan 4.2, wanda aka ƙiyasta darajar sa ta kai kusan dala miliyan 336, kwanaki kaɗan bayan kama mafi girman miyagun ƙwayoyi a tarihin ƙasar.

Hukumomin ƙasar sun bayyana cewa bincike ya gano wasu jami’an ‘yan sanda da ake zargi da taimakawa wajen jigilar hodar iblisin bayan shigowar ta ƙasar, daga cikin waɗanda ake tuhuma akwai shugaban rundunar sintirin manyan hanyoyi da kuma shugaban sashen manyan laifuka na ‘yan sanda.

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Liberia, Gregory O.W. Coleman, ya ce an kama wani mataimakin kwamandan ‘yan sanda a babban filin jirgin saman ƙasar cikin waɗanda ake zargi yayin da ake ci gaba da bincike.

A makon da ya gabata, hukumomin Liberia sun sanar da kama kusan tan 4 na hodar iblis mai darajar da ta kai kusan dala miliyan 317, inda suka ce an gano hanyar safarar miyagun ƙwayoyin ta ƙasa da ƙasa tare da kama wasu ‘yan ƙasar waje biyu da ake zargi da hannu.

Ma’aikatar Shari’a ta Liberia ta ce an gano hodar ne yayin wani samame a wani gida da ke yankin Duazon, mai tazarar kilomita 28 daga babban birnin ƙasar Monrovia, an kama wani ɗan ƙasar Serbia da kuma wani mutum ɗan ƙasar Colombia da Spain.

Ƙasashen yammacin Afirka na ƙara zama hanyar masu safarar hodar iblis daga Kudancin Amurka zuwa Turai, inda masu safarar ke amfani da rashin tsaro a wasu yankuna.

Wata Kungiya dake yaƙi da manyan laifuka wato Global Initiative Against Trans-national Organized Crime ta ce kaso da yawa na hodar iblisin da ake kaiwa Turai na wucewa ta yankin Africa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *