Tawagar Super Falcons ta Najeriya za ta yi ƙoƙarin dawo da martabar kare kambun ta na Gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta Mata (WAFCON) lokacin da za ta fafata da Zambia a wasan rukuni na C a filin wasa na Stade Larbi Zaouli da ke Casablanca, a Moroko, ranar Asabar.
Super Falcons sun fuskanci ɗaya daga cikin manyan abubuwan mamaki na gasar a wasansu na farko, inda suka sha kashi ci 3-2 a hannun Malawi duk da cewa sune masu riƙe da kofin.
Tawagar Justin Madugu ta sha matuƙar wahala a hannun Temwa da ‘yar uwarta Tabitha Chawinga, inda Temwa ta zura ƙwallo 2, ita kuwa Tabitha ta zura ƙwallar da ta tabbatar da nasarar doke Super Falcons a wasan.
-
WAFCON 2026: Yadda Algeria da Kenya suka sha kaye a hannun Moroko da Senegal
-
WAFU B U20: Flying Eagles sun lallasa Sparrow Hawks da ci 3-0
-
UEFA ta yi barazanar ƙaurace wa gasar cin Kofin Duniya idan FIFA ta…
Ƙalubalen da ke gaban Najeriya ya ƙara zama mai wahala yayin da za ta fafata da tawagar Zambia wadda Barbra Banda ke jagoranta.
’Yar wasan ta taka rawar gani yayin da Zambia ta doke Egypt da ci 6-0, inda ta zura kwallaye 4 don tabbatar da matsayin na ɗaya daga cikin ’yan wasa mata masu haɗari a Afirka.
Barbra Banda ta Zambia ta zura kwallaye 32 tare da bayar da taimakon 4 a wasanni 21 na wasannin kasa da kasa.
Wasan na ranar Asabar zai kuma baiwa Zambia damar ɗaukar fansa bayan shan kashi da ci 5-0 a hannun Najeriya a wasan Kwata-fainal na WAFCON na bara.
Sai dai har yanzu Najeriya ce ƙasar da ta fi kowacce cin nasara a tarihin ƙwallon ƙafar mata ta Afirka, inda ta lashe kofin nahiyar sau 10 inda take sa ran sake lashe gasar karo na 11 a bana.
