Sanata Shehu Buba Umar ya ce bai taɓa ɗaukar nauyi ko samar da kudin gudanarwa ko ba da makamai, ko sauƙaƙawa, ko tallata ayyukan ‘yan bindiga da ta’addanci da garkuwa da mutane, ko wata ƙungiyar laifuka ko ayyukan ta’addanci ta kowace hanya ba.
Sanata Buba ya bayyana haka ne a ranar Litini a wani taron manema labaru da ya kirawo don wanke kan sa bisa zarge-zargen daukar nauyin ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane da ake yi masa.
Buba, wanda, ya ce ba shi da abin ɓoyewa kuma ba sgi da abin tsoro daga kowane bincike na doka, ya ce ya mika kan sa ga Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS) da ‘Yansanda, da DIA domin a gudanar da cikakken bincike mai zurfi kan kowane zargi da aka yi a kan sa.
A cewarsa, lauyoyinsa sun rubuta wasiƙa a hukumance zuwa ga DSS da DIA, da ‘Yansanda, suna buƙatar cewa hukumomin su binciki waɗannan zarge-zarge domin muradun tsaron ƙasa da kariya ga mutuncisa da aminci sa a matsayina na ɗan Najeriya.
- Tinubu ya bayar da umarnin sakin kudaden da aka ware wa hukumomin raya yankuna
- Gwamnatin Kaduna ta kwato hekta 500,000 na gonakin da ‘yan bindiga suka mamaye
- Rikicin Hormuz: Farashin litar man fetur ya kai 1,430 a Abuja
Sanata Buba yace ya ɗauki wannan mataki ne saboda bai yarda cewa zarge-zargen ta’addanci da ayyukan bindiga, da garkuwa da mutane a kan wani Sanata mai ci a Jamhuriyar Tarayyar Najeriya ya kamata su zamanto abubuwan jita-jita a shafukan sada zumunta ba.
Ya ce waɗannan laifuka ne masu girma; ya kamata a bincike su da mahimmanci.
“Sakamakon haka, ina gayyatar kowa a fili—yan siyasa, masu fafutuka, masu tasiri a shafukan sada zumunta, ‘yan jarida, ko kowane ɗan Najeriya da ke da shaidar kwarai cewa na ɗauki nauyi, samar da kudi, ba da makamai, sauƙaƙawa, ko tallata ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane, ko kowace ƙungiyar laifuka—da ya kai wannan shaida zuwa ga hukumomin tsaro da abin ya shafa. Kada ku ɓuya a bayan shafukan sada zumunta. Kada ku dogara ga bidiyoyin da aka yi wa gyara, ƙagaggun labarai, faɗan farfaganda, ko zarge-zargen da ba a san tushensu ba. Ku kai kowace shaida da kuke da ita zuwa ga hukumomin tsaro da suka dace kuma ku bar doka ta yi aikinta”, in ji shi.