Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da rushe Kwamitin Shugaban Kasa ta Musamman Mai Sa Ido akan Siyar da Daukakar Jari na Gwamnatikin Tarayya (PIC) cikin gaggawa.

Wata sanarwa da Bayo Onanuga, Mai Bada Shawara na Musamman ga Shugaban Kasa Kan Labarai da Tsare-tsare ya sanya wa hannu ta ce daga yanzu, duk wani al’amari da ya shafi ayyukan wannan kwamiti, Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (HAGF), ne zai kula da shi.

An kafa hukumar PIC ne a shekara ta 2000 lokacin gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo domin ta kula da mayar da hannun jari ga masu zaman kansu, siyarwa, da kuma bada hayar filaye da gine-gine na Gwamnatikin Tarayya a karkashin tsarin canza kadarori zuwa kudi na gwamnati.

Mambobinta sun hada da Ministan Gidaje na wancan lokacin a matsayin Shugaba, tare da wakilai daga Ma’aikatun Sufuri da Shari’a da Lafiya da Noma da kuma Hukumar ‘Yan Sandan Najeriya.

Farfesa P.T Ahire, wanda a lokacin yake matsayin Mataimakin Darakta a Ofishin Sakataren Gwamnatikin Tarayya, shi ne ya kasance Sakataren farko. Sauran mambobin an zabo su ne daga bangarorin gwamnati da masu zaman kansu.

A ranar 22 ga watan Maris, 2001, Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da kafa Kwamitin Bincike domin samar da kwamitin.

Kwamitin ya yi aiki na tsawon watanni 21 kafin ya mika rahotonsa.

Bayan tsanake, Gwamnati ta lura cewa ayyukan PIC sun wuce iyakokin ainihin aikin da aka ba su, wanda hakan ya haifar da shari’o’i da dama a kotuna daban-daban na kasar nan, kuma ci gaba da kasancewar kwamitin ba shi da wani amfani kuma.

Sakamakon haka, Shugaban Kasa ya ba da umarnin rushe PIC kuma Babban Lauyan Tarayya ya karbi ragamar ayyukansu fara daga ranar 5 ga watan Nuwamba, 2025.

Bayan wannan umarni na Shugaban Kasa, PIC ta rushe, kuma an umarci tsohon Sakatare, B. S Dutsin-Ma, da ya daina duk wani aiki a madadin kwamitin da kuma Gwamnatikin Tarayya akan abubuwan da suka shafi wannan batu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *