Tawagun maza da na mata na Najeriya sun samu gurbin shiga Gasar cin Kofin Ƙwallon Kwando ta ƙasashen Afirka ta 2026 bayan samun kyakkyawan nasara a wasannin CAVB Zone 3 da aka gudanar a Abidjan, da ke Cote d’Ivoire.

Tawagar maza ta Najeriya za ta buga gasar nahiyar da za a gudanar a Kenya, yayin da tawagar mata za ta buga a gasar da za a gudanar a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.

Samun wannan guraben ga tawagun biyu babban nasara ne ga wasan ƙwallon kwando na Najeriya biyo bayan nuna ƙwazo a wasannin sharen fage na nahiyar da suka fafata da wasu manyan ƙasashen Afirka.

Samun gurbin ya kuma nuna ci gaban da wasan ƙwallon kwando na Najeriya ke yi a hankali. A halin yanzu, tawagar maza ta Najeriya tana matsayi na 52 a sabuwar jerin matsayi na duniya na FIVB, yayin da tawagar mata ke matsayi na 103 a duniya.

Gasar ƙwallon kwando ta ƙasashen Afirka ta 2026 za ta hada manyan ƙasashe na nahiyar, yayin da Najeriya ta ƙudiri niyyar yin tasiri mai karfi a gasar maza da ta mata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *