Ɗan damben Birtaniya, Anthony Joshua, ya tuna da marigayi abokansa da suka rasu a hatsarin mota a Najeriya bayan ya kaucewa shan kaye a hannun Kristian Prenga a fafatawar da suka yi a daren ranar Asabar a Jeddah.
Joshua ya kuma tabbatar da cewa zai fafata da Tyson Fury wanda ya ce za ta zama “kyakkyawar kyauta” ga magoya baya.
Joshua ya doke ɗan damben na Albaniya, Prenga, a zagaye na biyu bayan da Prenga din ya kai shi kasa sau biyu a zagaye na farko.
Sai dai Joshua ya doke Pregna a dakika 20 kacal bayan fara fafatawar zagaye na biyu.
-
Super Falcons ta fitar da sabuwar rigarta mai taurari 10 kafin Gasar WAFCON ta 2026
-
Gwamna Sule ya bai wa Nasarawa Amazons da sauran ƙungiyoyin wasanni kyautar kuɗi da mota
-
Gwamnatin Tarayya ta baiwa tawagar ‘yan wasan ɗaga nauyi na masu buƙata ta musamman kyautar kuɗaɗe
Tauraron Birtaniyan ya nuna ƙarfin hali, ƙwazo da juriya yayin fafatawar.
Wannan dabi’a ta kasance tare da shi tun bayan rasuwar abokan tawagarsa, Sina Ghami da Latif ‘Latz’ Ayodele, a wani hatsarin mota a watan Disamba da ya faru da shi yana cikin motar.
Da yake zantawa da kafar DAZN bayan ya doke Prenga, Joshua ya ce “Nasara a kan Prenga ta tabbatar da cewa Joshua zai fafata da Tyson Fury a fafatawar da magoya baya ke jira cikin zumudi.
