‘Yan wasan Najeriyar da suka lashe lambobin yabo sun samu kyautar kuɗaɗe, bayan bajintar da suka nuna a wasannin motsa jiki na ƙasashe rainon Ingila da ke gudana a birnin Glasgow, na Scotland.
Shugaban Hukumar Wasanni ta Ƙasa (NSC), Shehu Dikko, ya sanar da cewa ‘yan wasan da suka samu lambar yabo za su samu kyautar kuɗi nan take ta cikin asusun ajiyar su.
Ɗan wasa Roland Ezuruike, wanda ya samu lambar azurfa a gasar ɗaga nauyi ta Maza a rukunin A, ya samu kyautar Dala dubu 5.
-
Super Falcons za ta fara kare kambunta na WAFCON akan Malawi ranar Lahadi
-
Jamus ta naɗa Jurgen Klopp a matsayin sabon kocin Tawagar Kasar
-
Gasar cin Kofin Duniyar da ba Najeriya a ciki, ba cikakke ba ne – Shugaban CAF Motsepe
A ɓangaren mata kuwa, ƴar wasa Esther Nworgu ce ta lashe lambar zinare a gasar ɗaga karfe mai nauyi ta Mata, inda ta samu kyautar Dala dubu 10.
Ita kuwa ƴar wasa Esther Onyema, wadda ta samu lambar azurfa, ita ma ta samu kyautar Dala dubu 5.
‘Ƴan wasan dai sun tashi da wani adadi na kuɗaɗen a hannu su, yayin da aka tura musu ragowar ta cikin asusun ajiyar su kamar yadda Gwamnatin Najeriya ta alƙawar ta.
Bisa dukkan alamu tawagar Najeriyar ta fara gasar da ƙafar dama, inda take kan matsayi na biyu a teburin gasar, wadda aka fara ranar Jumma’a 24 ga watan Yulin 2026.