Tawagar 'yan wasan Super Falcons

Super Falcons ta Najeriya za ta fara kare kambunta na Gasar cin Kofin Mata ta Afirka, WAFCON, ta 2026 akan Malawi a ranar Lahadi a ƙasar Moroko.

Najeriya na fatan sake lashe kofin na nahiyar Afirka a karo na 11 bayan ta lashe gasar sau 10.

Za a fara gasar ne daga ranar 26 ga Yuli zuwa 16 ga Agusta, inda ƙasashe 16 za su fafata domin lashe kofin Gasar ƙwallon ƙafa ta mata ta Afirka.

Najeriya, wadda ke riƙe da kambun ta na cikin Rukuni na C tare da Zambia, Masar da Malawi.

Super Falcons za su buga da Malawi a wasan su na farko a ranar 27 ga Yuli, sannan su buga da Zambia a ranar 31 ga Yuli, kafin Masar a ranar 4 ga Agusta.

Kocin tawagar Super Falcons, Justin Madugu, ya ce tawagar sa ta ƙara mayar da hankali duk da cewa ta na da tarihi mai kyau a gasar.

“Mun san yanzu kowace tawaga na ganin za ta iya ƙalubalantar Najeriya. Dole ne mu tabbatar da samun nasara ta hanyar ƙara kwazo da ladabi, da jajircewa,” in ji shi.

Wannan gasar kuma wani bangare ne na tantancewar shiga Gasar cin Kofin Duniya ta mata ta 2027 da za a yi a Brazil.

Ƙasashe 4 da za su kai wasan kusa da na karshe za su samu tikitin shiga Gasar cin Kofin ta Duniya kai tsaye.

Har ila yau, Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta nahiyar Afirka, CAF, ta kuma ƙara kudin kyautar gasar.

Zakarar gasar za ta samu dala miliyan 2, yayin da jimillar kuɗaɗen da za a bayar kyauta ya kai dala miliyan 5.8. inda kowace ƙasa da ta shiga shiga gasar za ta samu dala 150,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *