Super Falcons

Super Falcons ta Najeriya za ta samu ɗudi dala miliyan 2 idan ta lashe Gasar cin Kofin mata ta Afirka ta 2026 da za a buga a Moroko.

Wannan shine mafi girman la’ada ga ƙasar da za ta lashe gasar a tarihi.

Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka, CAF, Patrice Motsepe, shi ya sanar da ƙarin kuɗin a ranar Laraba yayin Taron CAF da aka gudanar a Johannesburg, Afirka ta Kudu.

Ana sa ran wannan sabon la’ada zai ƙara wa ƙasashe ƙwarin gwiwa sa’an nan kuma zai bunƙasa ƙwallon ƙafa ta mata a nahiyar Afirka.

Super Falcons za ta shiga gasar ne a matsayin ɗaya daga cikin manyan ‘yan takara, domin su ne suka lashe gasar na ƙarshe da aka buga a Moroko.

Baya ga fafutukar lashe kofin nahiyar, ƙasashe ɗudu da za su kai wasan kusa da na ƙarshe za su samu tikitin shiga Gasar cin Kofin Duniya ta mata ta 2027 kai tsaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *