Phil Foden, dan wasan Ingila da Man City

Ɗan wasan tsakiya na Manchester City, Phil Foden, ya sanya hannu kan sabon kwantaragn shekara 4 wanda zai zaunar da shi a ƙungiyar har zuwa 2030.

Ɗan shekara 26, wanda dama kwantiraginsa zai ƙare a bazara mai zuwa ya zaɓi tsawaita zamansa a ƙarƙashin sabon kocin, Enzo Maresca.

Foden ya fara buga wa tawagar manya na ƙungiyar tun yana da shekara 17 zamanin koci Pep Guardiola. Tun daga lokacin ya buga wa City wasanni 369 inda ya lashe kofunan gasar Firimiyar Ingila 6, da na Zakarun Turai 1, da kuma FA Cup 2.

“Ci gaba da zama a City na nufin komai a gare ni. Buga wa wannan ƙungiyar wasa shi ne abin da na yi mafarki tun ina ƙarami, kuma girmamawa ce gare ni ko yaushe in saka rigar wannan ƙungiya,” in ji Foden.

A kakar da ta wuce Foden ya zura ƙwallaye 7 kuma ya taimaka da 5 a wasanni 33 na gasar Firimiyar Ingila. A kakar da ta gabata kuma ya zura 7 ya taimaka da 2 a wasanni 28.

Foden, wanda shi ne ɗan wasan City da ya fi kowa samun kofuna tare da John Stones da Bernardo Silva, ya buga duk wasanninsa na City a ƙarƙashin Guardiola, wanda ya shafe shekaru 10 a ƙungiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *