Jam’iyyar APC ta yi watsi da zargin Atiku Abubakar, na cewa an ware kuɗaɗen Service-Wide Vote (SWV) na kasafin kuɗin shekarar 2026 domin tallafa wa yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Jam’iyyar ta bayyana cewa Service-Wide Vote (SWV) wata hanya ce da aka daɗe ana amfani da ita a tsarin kasafin kuɗin gwamnati domin biyan buƙatun da ka iya tasowa bayan an amince da kasafin shekarar.
Jam’iyyar APC ta ce tana mamakin yadda Atiku, wanda ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin shugaban Ƙasa, ya yi irin wannan zargi duk da cewa ya kamata ya fahimci yadda tsarin kasafin kuɗin gwamnati ke aiki.
Jam’iyyar APC ta ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da nuna gaskiya da kula da kuɗaɗen jama’a ta hanyar aiwatar da shirye-shirye daban-daban. Ta ambaci Asusun Lamunin Ilimi na Ƙasa (NELFUND), wanda a cewar ta ya taimaka wa kusan ɗalibai miliyan biyu samun damar karatu a manyan makarantu, da aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi.
- FRSC ta gano motocin da ake zargin an sace su biyu a Edo ta hanyar NVIS
-
Obi ya amince zai yi wa’adi ɗaya idan aka zaɓe shi — Kwankwaso
APC ta kuma ce gwamnati na ci gaba da ƙara saka hannun jari a fannonin gine-ginen more rayuwa, kiwon lafiya, noma, samar da ayyukan yi da kuma gyaran tsarin haraji domin bunƙasa tattalin arziki da rage nauyin haraji ga masu ƙaramin ƙarfi.
A ƙarshe, jam’iyyar ta ce gwamnatin Shugaba Tinubu za ta ci gaba da aiwatar da manufofin Renewed Hope Agenda da nufin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa, ƙarfafa cibiyoyin gwamnati, faɗaɗa ayyukan more rayuwa da kuma inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
Sai dai Atiku Abubakar bai fitar da martani kan wannan sanarwar ta APC ba a lokacin haɗa wannan rahoto.