Hukumar Kula da Kare Haɗurra ta Ƙasa FRSC ta gano wasu motoci biyu da ake zargin an sace su a jihar Edo ta hanyar amfani da tsarin tantance motoci na NVIS.
Motar farko ita ce Toyota Highlander, inda binciken NVIS ya nuna cewa lambar rajistar da ke jikin motar ba ta dace da bayananta ba. Bayan amfani da lambar tantance mota ta musamman (VIN), an gano cewa an sace motar a Legas a watan Yunin 2025.
A wani bincike na daban, jami’an FRSC sun gano wata Toyota Venza wadda aka kawo domin tantancewa ba tare da lambar rajista ba. Binciken ya gano ainihin bayananta, inda mai ita ya tabbatar cewa an rasa motar tun watan Janairun 2026 a Sapele, jihar Delta.
- NNPP ta ɗora sunayen ‘yan takarar ta a shafin INEC
- Amurka za ta gina wa Saudiyya cibiyar Nukiliya marar hadari
Hukumar FRSC ta miƙa motocin biyu da waɗanda ake zargi zuwa sashen binciken manyan laifuka na ‘yan sandan jihar Edo domin ci gaba da bincike.
Shugaban FRSC, Shehu Mohammed, ya ce wannan nasarar ta nuna muhimmancin tsarin NVIS wajen gano motocin sata da tabbatar da mallaka da kuma yaƙi da laifukan da suka shafi motoci.