Ƙasashen AES da suka hadar da Burkina Faso, Mali da Nijar sun bayyana aniyar su ta haɗin gwiwar karɓar baƙuncin Gasar cin Kofin kasashen Afirka ta 2032.
Ƙasashen sun miƙa takardar nuna sha’awar ne ga Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka, CAF, wanda hakan shine mataki na farko na tsarin neman karɓar baƙunci.
An gabatar da buƙatar ne bayan ganawar wakilan ƙasashen 3 da Shugaban CAF, Patrice Motsepe, a Amurka yayin kammala Gasar cin Kofin Duniya ta 2026.
-
Anthony Taylor ya yi ritaya daga alƙalancin wasa
-
Guardiola na tattaunawa don zama sabon kocin Italiya
-
Sifaniya ta samu dala miliyan 50 a matsayin zakaran Kofin Duniya
Sai dai miƙa takarda ba ya nufin an sahale musu domin CAF bata fara tantance ƙasashen da suka miƙa buƙatar karɓar baƙuncin gasar ba.
A farkon wannan watan ne CAF ta buɗe ƙofar nemar shirya gasar AFCON na 2028, 2032 da 2036, inda ta gayyaci ƙasashe 54 da ke ƙarƙashinta su mika buƙatarsu.
Idan ƙasashen suka yi nasara, gasar za ta koma Burkina Faso da Mali a karo na farko tun bayan da suka shirya ta a 1998 da 2002, yayin da Nijar za ta karɓi baƙuncin AFCON a karon farko a tarihin ta.
