Alƙalin wasan kwallon kafa na duniya Anthony Taylor, ya sanar da ritayar daga fagen alƙalancin wasa nan take.
Taylor ya shafe tsawon shekaru 20 ya na alkalancin wasanni da suka hadar da gasar firimiyar Ingila, da gasar cin kofin duniya da Hukumar Ƙwallon Ƙafa FIFA ke shiryawa, da kuma wasanni daban-dabam.
“Ina son na bayyana godiya na ta musamman ga mataimakana biyu Gary da Adam, abokan aikina na alkalanci, da kuma duk wanda ya bani gudumuwa tsawon shekaru,” Inji Taylor.
-
Guardiola na tattaunawa don zama sabon kocin Italiya
-
Sifaniya ta samu dala miliyan 50 a matsayin zakaran Kofin Duniya
-
Najeriya ta sauka zuwa mataki na 4 a Afirka – FIFA
Dan shekaru 47, ya yi alkalancin wasan ƙarshe a ranar 6 ga Yuli, wasan da Sifaniya ta doke Portugal da ci 1-0 a zagaye na 16 na Gasar cin Kofin Duniya ta 2026.
Taylor ya yi alƙalancin wasanni 831, ciki har da wasanni 432 na gasar Firimiyar Ingila.
Taylor ya yi alkalancin wasannin karshe na League Cup na 2015, wasannin karshe na FA Cup na 2017 da 2020.
Sai kuma wasan karshe na UEFA Nations League na 2021 tsakanin Faransa da Sifaniya, da kuma wasan karshe na Europa League na 2023, inda Sevilla ta doke Roma a bugun fanareti.
