A karon farko da Amurka ta sake ƙaddamar sabbin hare-hare kan Iran, an sake kunna na’urorin kariyar sararin samaniya a babban birnin ƙasar, Tehran

A yankin arewa maso gabashin birnin, an ji ƙarar fashe-fashe a daren Talata, kamar yadda wani rahoto na kamfanin dillancin labarai na DPA ya bayyana.

A daidai lokacin da aka ji fashe-fashen a Tehran, sojojin Amurka sun sanar da cewa sun ƙaddamar da sabbin jerin hare-hare kan wuraren soji a Iran

Kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran ma sun ruwaito cewa an harba makaman kariya daga hare-haren sama a sassa daban-daban na Tehran, birnin da ke da mazauna kusan miliyan 15.

Sai dai jim kaɗan lamarin ya lafa, sannan sojojin Amurka suka sanar da kammala wannan sabon jerin hare-hare.

A cewar sanarwar Rundunar Sojojin Amurka (CENTCOM) da aka wallafa a shafin X, hare-haren sun kasance ne domin ragewa Iran ƙarfin kai hare-hare kan jiragen kasuwanci da ke bi ta mashigar Hormuz, muhimmiyar hanyar jigilar mai ta duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *