Rahotanni na nuni da cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya amince da wata yarjejeniya ta makamashin Nukiliya da Saudiyya.

A cewar rahoton jaridar The Wall Street Journal, yarjejeniyar za ta taimaka wa Saudiyya wadda ta daɗe tana takun-saƙa da Iran wajen gina cibiyar makamashin Nukiliya marar hadari.

Haka kuma, wani bangare na yarjejeniyar na bayyana cewa Saudiyya ka iya samun damar tace sinadarin uranium a cikin ƙasar ta, domin amfanin masana’antu da bukatar al’umma.

Rahoton ya ce yarjejeniyar, wadda aikin ginin cibiyar ka iya lashe biliyoyin daloli, za ta yi aiki na tsawon shekaru 30.

Haka kuma za ta tabbatar da cewa kamfanonin Amurka ne za su taka muhimmiyar rawa wajen gina cibiyoyin sarrafa makamashin, tare da hana sauran kamfanonin ƙasashen waje shiga wannan aiki.

A cewar gwamnatin Trump, wannan tanadi zai baiwa Amurka damar sa ido kan shirin nukiliyar Saudiyya tare da tabbatar da cewa ba za a karkatar da shi zuwa ayyukan soja ba.

Tun a watan Afrilun 2025, Sakataren Makamashi na Amurka, Chris Wright, ya fara tattaunawa da Saudiyya kan wannan yarjejeniya yayin wata ziyara da ya kai yankin.

A lokacin ne aka bayyana cimma sabuwar yarjejeniyar makamashi tsakanin Amurka da Saudiyya na iya buɗe hanya ga kafa shirin mallakar makamashin nukiliya marar hadari ga ƙasar Saudiyya.

Rahotanni sun ce ana iya sanya hannu kan yarjejeniyar  a ranar Laraba 22 ga watan Yulin shekarar 2026.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *