Kotun Shari’a ta Al’umma ta Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta ƙaddamar da Tsarin Gudanar da Shari’a ta Yanar Gizo (Electronic Case Management System – ECMS) domin mayar da hanyoyin shari’a tsarin na’ura mai ƙwaƙwalwa, inganta hanyoyin samun adalci, da kuma bunƙasa ingancin gudanar da shari’o’i a fadin ƙasashe mambobinta 15.

An ƙaddamar da dandalin ne a hukumance a birnin Abuja jiya, yayin wani biki da ya samu halartar manyan jami’an ECOWAS da alƙalai da jikokin jakadanci da lauyoyi da ƙungiyoyin farar hula, da kuma abokan hulda na ci gaba.

Ƙaddamarwar ta kasance wani babban mataki a tsarin sauya kotun zuwa amfani da fasahar zamani, inda aka sauya hanyoyin amfani da takardu zuwa wani dandali mai tsaro na yanar gizo wanda ke aiki da harsuna da dama domin shigar da kara, gudanarwa, da kuma bibiyar shari’o’i.

An tsara dandalin ECMS din ne domin tafiyar da ayyukan shari’a da na rajista ta hanyar na’ura mai ƙwaƙwalwa, wanda ke damar shigar da ƙara ta yanar gizo da adana takardu a tsarin na’ura da yin sauraron shari’a ta bidiyo (virtual hearings) da aika sanarwa ta yanar gizo, da kuma sa ido a kan tafiyar da shari’a a ainihin lokacin da ake yinta (real-time).

Dandalin yana samuwa ne a cikin harsunan Turanci da Faransanci, da kuma Harshen Potugal, wanda hakan ke saukaka amfani da shi ga lauyoyi da masu shari’a a fadin shiyar ECOWAS.

Yayin da yake jawabi a wurin taron, Shugaban Kotun ECOWAS, Mai Shari’a Ricardo Cláudio Monteiro Gonçalves, ya bayyana kaddamarwar a matsayin wani muhimmin lokaci a tarihin kotun shiyar, kuma babban mataki na karfafa samun adalci ga sama da ‘yan kasa miliyan 400 a cikin al’ummar ECOWAS.

Ya ce gabatar da wannan dandali yana nuna kudurorinsu na rungumar fasahar zamani wajen gudanar da ayyukan shari’a cikin sauri, gaskiya, da kuma nagarta.

“Mun taru, ido-da-ido a Abuja da kuma ta yanar gizo a fadin dukkan shiyar ECOWAS, domin alamar farkon wani sabon zamani wanda fasaha ke karfafa samun adalci, inganta aiki, da ciyar da gaskiya gaba a harkar shari’a, domin amfanin ‘yan kasa sama da miliyan 400,” in ji shi.

Mai Shari’a Gonçalves ya bayyana cewa tun lokacin da aka kafa ta, Kotun ECOWAS ta ci gaba da jajircewa wajen haɓaka tsarin mulkin doka, kare haƙƙoƙin ɗan adam, da tabbatar da ingantaccen fassarawa da aiwatar da dokokin Al’umma.

A cewarsa, kotun ta rika neman hanyoyin tabbatar da cewa adalci ya kasance mai ‘yanci, tsaka-tsaki, mai sauƙin samu, kuma yana amsawa ga sauye-sauyen duniya ta hanyar zamani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *