Gwamnatin kasar Afirka Kudu ta yi watsi da bukatar Najeriya ta neman biyan diyya ga ‘yan ƙasarta da suka yi watsi da sana’o’insu da dukiyoyinsu bayan sun gudu daga sabbin hare-haren ƙin jinin baƙi (xenophobia) da aka sake ƙaddamarwa a ƙasar.

Kwanan nan Najeriya ta bayyana cewa tana tattara alƙaluman sana’o’i, gidaje, da sauran dukiyoyin da ‘yan ƙasarta da abin ya shafa suka bari, domin amfani da su wajen tattaunawa da gwamnatin Afirka Kudu kan yiwuwar biyan diyya.

A farkon wannan mako, Maƙaddashin Babban Kwamishinan Najeriya a Afirka Kudu, Temitope Ajayi, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta soma rubuta asarar da ‘yan Najeriya da suka koma gida suka tafka sakamakon hare-haren.

Ajayi ya ce wannan tsari yana da nufin sauƙaƙa tattaunawa da hukumomin Afirka Kudu domin biyan diyya ga wadanda aka tilasta wa barin zuba jarin da abubuwan neman abincinsu saboda fargabar tsaro.

Sabanin haka, Minista a Fadar Shugaban Kasar Afirka Kudu, Khumbudzo Ntshavheni, ta yi watsi da wannan shawara yayin wani taron manema labarai a ranar Juma’a, inda ta jaddada cewa gwamnatin Afirka Kudu ba za ta biya kowa diyya kan dukiyoyin da aka bari baya ba.

A cewar Ntshavheni, dukiyoyin da aka mallaka ta hanyar doka suna da rajista a hukumance tare da hukumomin da abin ya shafa kuma ana iya sayar da su ta hanyar kasuwar dukiya ta ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *