Tawagar Falconets ta Najeriya ta lallasa ƙasar New Caledonia da ci 10-1 a wasan ƙarshe na rukunin F na Gasar Cin Kofin Duniya na Mata ‘yan ƙasa da shekaru 20 da suka buga a ranar Lahadi, a ƙasar Poland.
Falconets ta samu damar tsallakawa zuwa zagaye na 16 bayan ta haɗa maki 4 daga wasanni uku da ta buga.
Ramotalahi Kareem da Onajite David, kowannen su, ta ci kwllo uku-uku, sannan kuma Rebecca Adegbemile ta ci ƙwallo biyu, sai kuma Janet Akekoromowei ta ci ƙwallo ɗaya, da kuma Tosin Rafiu ƙwallo ɗaya.
-
Chelsea ta yi wa Manchester United wankin babban bargo da ci 5-0
-
Najeriya ta miƙa buƙatar karɓar baƙuncin Gasar Motsa Jiki ta Duniya ta 2030
-
Arsenal ta casa Sunderland
‘Yar wasa Joceline Kourevi ce ta ci wa New Caledonia ƙwallo ɗayan da ta ci a minti na 89.
Spaniya ce ke matsayi na farko a rukunin na F bayan ta doke China da ci 3-1.
Spaniya, da Najeriya, da kuma China duk sun tsallaka zuwa matakin zagaye na 16, yayin da New Caledonia ta fice bayan ta sha kashi a wasanni uku a jere.
Falconets ta sha wahala a farkon wasan, inda ta fara da yin rashin nasara da ci 2-0 a hannun Spaniya a wasanta na farko, sannan kuma ta tashi 0-0 da China.
Yanzu Najeriya tana jiran a kammala wasannin rukuni na E domin sanin wadda za ta zama abokiyar fafatawarta a zagaye na 16 da kuma sanin jadawalin wasan.
