São Tomé – Shugaban ƙasar São Tomé da Príncipe mai ci, Carlos Vila Nova, zai kara da abokin hamayyarsa daga jam’iyyarsa, Nito Viegas D’Abreu, a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa, tare da wasu ‘yan takara biyu masu zaman kansu.

Viegas D’Abreu, wanda ɗan majalisar dokoki ne, ya samun goyon bayan tsohon Firayim Minista Patrice Trovoada, wanda yanzu ke jagorantar jam’iyyar Independent Democratic Action (ADI).

São Tomé da Príncipe, tsohuwar mallakar Portugal da ke Tekun Guinea, ƙasa ce mai yawan jama’a kusan 200,000. Duk da cewa ta taɓa fuskantar yunƙurin juyin mulki, ciki har da wanda aka yi a shekarar 2022, sojojin ƙasar sun dakile shi cikin gaggawa.

A tsarin mulkin ƙasar, shugaban ƙasa na da mafi yawan ayyukan wakilci da sanya hannu kan dokoki, yayin da babban ikon gudanar da gwamnati ke hannun Firayim Minista.

Vila Nova, mai shekaru 66, wanda aka zaɓa shugaban ƙasa a shekarar 2021 da goyon bayan jam’iyyar ADI, na bayyana kansa a matsayin jagoran da ya tabbatar da kwanciyar hankalin siyasar ƙasar

Sai dai ya sha suka bayan da ya sauke Patrice Trovoada daga mukamin Firayim Minista a watan Janairun 2025. Bayan shekara guda, kotu ta yanke hukuncin cewa matakin ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar

Trovoada, wanda ke neman komawa kan kujerar Firayim Minista a zaɓen ‘yan majalisar dokoki da za a gudanar a watan Satumba, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Nito Viegas D’Abreu

Shi kuwa D’Abreu, mai shekaru 43, na bayyana kansa a matsayin wakilin matasan da aka haifa bayan da ƙasar ta samu ‘yancin kai daga Portugal a shekarar 1975.

A gefe guda kuma, manyan kamfanonin mai na duniya, ciki har da Total Energies, sun samu lasisin gudanar da binciken yiwuwar haƙo man fetur da iskar gas a tekun da ke kewaye da tsibiran ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *