Mazauna jihohi shida a Arewacin Najeriya za su fuskanci katsewar wutar lantarki na tsawon kwanaki biyu sakamakon aikin gyaran kayayyakin aikin isar da wutar lantarki da Kamfanin dakon Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) zai gudanar.

A cewar kamfanin, za a dakatar da samar da wutar lantarki a ranakun Asabar da Lahadi domin bai wa injiniyoyi damar gudanar da aikin sabunta muhimman sassan layin wutar lantarki na ƙasa.

Jihohin da aikin zai shafa sun haɗa da Bauchi da Gombe da Yobe da Borno da Adamawa da Taraba.

A cikin wata sanarwa da Babbar Manajar Sashen Hulɗa da Jama’a ta TCN, Ndidi Mbah, ta fitar, ta ce an ɗauki matakin ne domin bai wa injiniyoyi damar girka kayan Optical Ground Wire (OPGW) a kan layin wutar lantarki mai ƙarfin 330kV daga Jos zuwa Bauchi da Gombe da ke tashar wutar lantarki ta Bauchi.

TCN ta bayyana cewa aikin wani ɓangare ne na shirin gwamnati wajen inganta tsarin dakon wutar lantarki, da ƙarfafa hanyoyin sadarwa da kuma ƙara amincin tsarin samar da wuta a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *