Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da manyan shirye-shirye biyar da Bankin Duniya ke tallafawa domin bunƙasa ilimi da rage talauci da inganta harkokin lafiya da ƙarfafa shugabanci da kuma faɗaɗa damar tattalin arziki a Najeriya.

Shirye-shiryen, waɗanda ke ƙarƙashin manufofin Renewed Hope na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, an ƙaddamar da su ne a ɗakin taro na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Shugaba Tinubu, wanda ya samu wakilcin Ministan Kuɗi da kula da Tattalin Arziki, ya ce shirye-shiryen sun nuna ƙudirin gwamnatinsa na mayar da sauye-sauyen tattalin arziki zuwa ingantacciyar rayuwa ga ‘yan Najeriya ta hanyar zuba jari a ilimi da lafiya da kariyar zamantakewa da gina ƙwararrun hukumomi

Ya jaddada cewa ilimi shi ne ginshiƙin ci gaban kowace ƙasa, yana mai cewa babu wata ƙasa da za ta kai ga ci gaba idan ba ta inganta tsarin iliminta ba

A nasa jawabin, Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, ya bayyana cewa shirin bunƙasa bil adama da wadata da daidaito ta hanyar Ingantaccen ilimin bai ɗaya (HOPE-EDU) zai samu tallafin kusan dala miliyan 552.18, wanda Bankin Duniya da Global Partnership for Education (GPE) suka haɗa kai wajen samarwa

Ya ce shirin zai amfanar da kusan yara miliyan 30 a faɗin Najeriya, tare da horas da malaman firamare na gwamnati 500,000 domin inganta ƙwarewarsu.

Shirye shiryen sun haɗa da inganta tsarin koyarwa da koyo a fiye da makarantun firamare na gwamnati 65,000, ƙarfafa tsarin gudanar da ilimi a dukkan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, taimaka wajen rage ƙarancin ilimi da inganta ƙwarewar malamai da ƙarfafa tsarin tattara bayanan ilimi da kuma tabbatar da amfani da bayanai wajen tsara manufofi da rabon albarkatu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *