Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja, na samun sauye-sauye masu kyau ƙarƙashin jagorancin Nyesom Wike a matsayin Minista, shekaru 50 bayan kafa babban birnin.

Tinubu ya bayyana hakan ne a Abuja a daren Juma’a yayin wani liyafar godiya ta musamman domin murnar kammalawa da ƙaddamar da ayyuka 31 a cikin kwanaki 28 a faɗin babban birnin

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, wanda ya wakilci shugaban ƙasa, ya yaba wa Wike da tawagarsa saboda ƙoƙarin da suka yi wajen tabbatar da cewa babban birnin ƙasar yana aiki yadda ya kamata domin amfanin dukkan ‘yan Najeriya.

Ya kuma yaba wa ministan, yana mai cewa ya nuna cewa: Ba yawan sanar da tsare-tsare ke nuna nagartar shugabanci ba, sai dai irin sakamakon da jama’a ke gani a aikace.”

Tinubu ya ce Abuja mallakin kowa ne ɗan Najeriya ne, yana mai bayyana ta a matsayin birnin da ke haɗa kan ƙasa, inda bambance-bambance ke haɗuwa, kuma inda buri da fata na kowane ɗan ƙasa ke samun matsuguni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *