Shugaba Bola Tinubu ya bai wa sabuwar Majalisar Kula da Harkokin Kuɗaɗen Dijital wa’adin kwanaki 30 domin ta samar da cikakken tsarin aiwatar da sabuwar dokar da ya rattaba wa hannu.

A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, sabon tsarin zai haɗa da gwajin sabbin kayayyakin kuɗaɗen dijital a ƙarƙashin kulawar Babban Bankin Najeriya (CBN), kafin a ba su damar shiga kasuwa gaba ɗaya.

Haka kuma, Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Ƙasa (NRS) za ta fitar da manufofin haraji ga masu harkokin kuɗaɗen dijital domin tabbatar da cewa fannin na ba da gudummawa ga kuɗaɗen shiga na gwamnati.

Gwamnatin Tarayya ta ce tana kuma kammala wani cikakken kundin manufofi kan harkokin kadarorin dijital, wanda zai zama jagora ga masu ruwa da tsaki da kuma ci gaban tattalin arzikin dijital a Najeriya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *