Gwamnatin Tarayya ta kafa Majalisar Kula da Harkokin Kuɗaɗen Dijital domin haɗa kai tsakanin hukumomin da ke sa ido kan kasuwar kadarorin dijital a Najeriya.
A ƙarƙashin sabon tsarin, Babban Bankin Najeriya (CBN) ne zai jagoranci majalisar, yayin da Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Ƙasa (NRS) da Hukumar Kula da Kasuwar Hannayen Jari (SEC) za su kasance mataimakan shugabanni.
Sauran mambobin majalisar sun haɗa da Hukumar Binciken Kuɗaɗen Sirri (NFIU) da kuma Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (ONSA).
- Abin da ya kamata ku sani game da Alkalin Wasan Karshe na Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026
- Ɓunƙasa Ilimi da rage talauci: Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirye-shirye biyar na bankin Duniya
Majalisar za ta tsara manufofi, ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin, tare da aiki da Babban Lauyan Tarayya wajen samar da tsarin doka guda da zai dace da manufofin tsaro da tattalin arzikin Najeriya.
A sanarwar da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce tsarin zai fara aiki nan take.
