Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta zabi dan kasar Slovenia, Slavko Vincic, ya ya yi alkalancin wasan karshe na Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026 wanda za a buga ranar Lahadi tsakanin Spaniya da Argentina.
Vincic, mai shekara 46 a duniya, ya zama alkalin wasa na farko daga kasarsa da zai jagoranci babban wasa a gasar duniya.
Jim kadan bayan samun labarin, Vincic ya ce ya yi mamaki da kuma farin ciki da zaben shi da FIFA ta yi domin ya jagoranci babban wasan.
-
FIFA ta fara horas da masu gudanar da harkokin ƙwallon ƙafa na mata a Abuja
-
Abdul Maikaba ya za ma sabon kocin Bayelsa United
-
Gasar Cin Kofin Duniya: Messi ya jagoranci Argentina zuwa wasan karshe bayan doke Ingila 2-1
“Da farko na yi mamaki. Sannan farin ciki ya biyo baya.
“Na yi rawa. Wannan girmamawa ce ta musamman samun damar jagorantar wasan karshe na Gasar Cin Kofin Duniya,” inji Vincic.
Ya kara da cewa, “Duk wani alkalin wasa yana mafarkin samun wannan dama. Ina alfahari da kaina da tawagata.
“Yana da wuya a bayyana komai cikin kalmomi, amma ina alfahari da wakiltar kasata, Slovenia, a taron wasanni mafi girma a duniya.
“Tawagata na alfahari, kuma za mu yi iya bakin kokarinmu.”
Abin da ya kamata ku sani game da Slavko Vincic
Wannan ne karo na biyu da Slavko Vinic yake alkalanci a Gasar Cin Kofin Duniya. A Gasar ta 2022 da aka yi a Qatar ya jagoranci wasanni biyu na rukuni.
A bana kuma, ya jagoranci wasan da Brazil ta buga da Morocco a rukunin C wanda aka tashi kunnen doki, da wasan da Algeria ta yi nasara a kan Jordan a rukunin J, da kuma wasan da Mexico ta yi nasara a kan Ecuador a zagayen ’yan 32.
Har wa yau, a 2024 UEFA ta nada shi ya jagoranci wasan karshe na Gasar Zakarun Turai a filin wasa na Wembley, inda Real Madrid ta doke Borussia Dortmund 2-0.
Haka kuma ya jagoranci wasan karshe na gasar Europa League a 2022, inda Eintracht Frankfurt ta doke Rangers a bugun fenareti ta dauki kofin.
