Lionel Messi ya sake jagorantar Argentina zuwa nasara mai ban mamaki bayan sun farfado daga baya suka doke Ingila da ci 2-1, suka tsallake zuwa wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya ta 2026.

Zakaran duniya za su samu damar kare kambunsu akan Spaniya a ranar Lahadi a New York a filin wasa New Jersey Stadiya.

Enzo Fernandez da kuma Lautaro Martinez ne suka ci ƙwallayen da suka juya akalan wasan, bayan Anthony Gordon ya fara daura Ingila kan gaba da kwallon da ya ci a minti na 55.

Rabin farko na wasan ya kasance mai tauri yayinda babu wata tawagar da ta samu damar kai harin cin ƙwallo.

Idanuwan duniya sun koma kan Messi, kuma bai baiwa kasar kunya ba inda ya samar da taimako guda biyu na kwallayen da Argentina ta ci wadda hakan ya sa ta tsallaka zuwa wasan ƙarshe da Spaniya.

Sai dai lamarin bai yi wa tawagar Ingila daɗi ba wadda wannan ne karo na biyu da ake cire su a wannan karni a matakin wasan kusa da na karshe na Gasar Cin Kofin Duniya bayan hakan ya faru da su a 2018 yayinda suka sha kaye a hannun Croatia da ci 2-1.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *