Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa EFCC ta samu nasara a shari’ar ƙwace kadarorin da ake alaƙanta wa da tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), bayan kusan watanni shida da ta fara shari’a.
Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci a ƙwace kadarori 48 tare da mayar da su hannun Gwamnatin Tarayya, bayan amincewa da buƙatar EFCC.
A cikin wata sanarwa, EFCC ta ce tun a ranar 6 ga Janairun 2026 ne ta fara samun umarnin wucin gadi na ƙwace kadarorin daga kotu, sannan ta wallafa sanarwa tana gayyatar duk masu ruwa da tsaki su bayyana dalilan da ya sa bai kamata a ƙwace kadarorin ba.
- Gasar Cin Kofin Duniya: Messi ya jagoranci Argentina zuwa wasan karshe bayan doke Ingila 2-1
- Majalisar Wakilai: Abbas ya ba da shawarwari kan yadda za a kafa ‘yan sandan Jihohi
Sai dai bayan sauraron ƙorafe-ƙorafen Malami da wasu mutum 14 da suka haɗa da ‘yan uwansa da abokan hulɗarsa, kotun ta tabbatar da ƙwace kadarorin baki ɗaya.
Daga cikin kadarorin da aka ƙwace akwai Jami’ar Rayhaan da ke Jihar Kebbi da Rayhaan Radio da otal-otal da gidaje da masana’antu da tashar mai da filaye a jihohin Kebbi da Kano da Babban Birnin Tarayya Abuja.
EFCC ta bayyana hukuncin a matsayin wani gagarumin ci gaba a ƙoƙarinta na ƙwato kadarorin da ake zargin an mallake su ta hanyar haramtacciyar hanya.