Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ce tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), da sauran waɗanda suka yi iƙirarin mallakar wasu kadarori 48 sun kasa gabatar da hujjojin da ke nuna cewa sun mallake su ne ta hanyar halastacciyar hanyar samun kuɗi.

Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta bayyana hakan ne yayin da take yanke hukuncin ƙwace kadarorin tare da mayar da su hannun Gwamnatin Tarayya.

Kotun ta ce Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gabatar da hujjojin da suka isa su nuna cewa ana zargin kadarorin sun samo asali ne daga haramtattun ayyuka, yayin da waɗanda ake ƙara suka gaza sauke nauyin da doka ta ɗora musu na bayyana sahihin asalin kuɗin da aka yi amfani da su wajen sayen kadarorin.

Mai shari’ar ta ƙara da cewa a irin wannan shari’ar ƙwace kadara, ba wai kawai mutum ya ce kadarar tasa ba ne ya isa, sai ya nuna hujjojin yadda ya mallake ta ta hanyar doka.

Hukuncin ya shafi kadarori 48 da suka haɗa da Jami’ar Rayhaan da Rayhaan Radio da otal-otal da gidaje da filaye da masana’antu da wasu kadarori da ke jihohin Kebbi da Kano da Babban Birnin Tarayya.

EFCC ta bayyana hukuncin a matsayin wata babbar nasara a yaƙin da take yi da cin hanci da rashawa da kuma ƙwato kadarorin da ake zargin an mallake su ba bisa ƙa’ida ba.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *