Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci a Najeriya (NSCIA), Mai Alfarma Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ayyana ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli, 2026, a matsayin ranar farko ta watan Safar 1448 bayan Hijira, biyo bayan rashin ganin jinjirin watan a faɗin Najeriya.
Wannan sanarwa ta zo ne bayan da Kwamitin Duban Watan Ƙasa da sauran kwamitocin duban wata na jihohi da na ƙananan hukumomi suka gaza samun sahihin rahoton ganin jinjirin watan Safar a ranar Talata, 14 ga watan Yuli, wadda ta yi daidai da ranar 29 ga watan Muharram 1448 bayan Hijira.
- Masu garkuwa da mutane sun sace shugaban makaranta, Jami’in NECO, da ɗalibai a Kogi
- Celtic ta yi wa Iheanacho tayin sabon kwantaragin shekara biyu bayan lashe kofin gasar
Sanarwar tana ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamitin Shura na Fadar Sarkin Musulmi Kan Harkokin Addini ya fitar ranar Laraba, wadda Shugaban kwamitin, Farfesa Sambo Wali Junaidu (Wazirin Sakkwato), ya sanyawa hannu.
A cewar sanarwar, rahotannin da aka karɓa daga kwamitocin duban wata na ƙasa baki ɗaya sun tabbatar da cewa ba a ga jinjirin watan da ke nuna farkon sabon watan Musulunci ba a ranar Talata, wanda hakan ya sa ya zama dole a cika kwanakin watan Muharram na yanzu zuwa talatin, daidai da koyarwar Musulunci.