Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da shugaban makarantar sakandaren gwamnati ta Government Secondary School, Odo-Ekina, jami’in ad-hoc na hukumar shirya jarrabawa ta ƙasa (NECO) guda ɗaya, da kuma ɗalibai huɗu lokacin da ake tsaka da gudanar da jarrabawar NECO a ƙaramar hukumar Dekina da ke jihar Kogi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, Salisu Oyiza, ta tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba. Ta bayyana cewa hararin ya auku ne da misalin ƙarfe 5:25 na yammacin ranar Talata yayin da ɗaliban ke tsaka da rubuta jarrabawa.
“A lokacin hararin, masu garkuwar sun yi awon gaba da ɗalibai huɗu, shugaban makarantar, da kuma ma’aikacin wucin gadi (ad hoc) na hukumar NECO guda ɗaya,” in ji Ms Oyiza.
Ta ƙara da cewa haɗin gwiwar rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun ƙaddamar da aikin bincike da ceto nan take.
Haka kuma, ta bayyana cewa zuwa yanzu an yi nasarar ceto ɗaya daga cikin ɗaliban da aka sace, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran mutanen da ke hannun masu garkuwar da kuma kamo waɗanda suka aikata laifin.
- Celtic ta yi wa Iheanacho tayin sabon kwangilar shekara biyu bayan lashe kofin gasar
- Manchester United na neman dan wasan gaban Arsenal
- ‘Yan sanda a Kano sun kama wanda ake zargi da kai wa ‘yan bindiga makamai a BichMinist
A cewar kakakin ‘yan sandan, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kogi, Naziru Kankarofi, tare da Kwamandan runduna ta 12 na rundunar sojin ƙasa ta Najeriya, da kuma Mai bai wa gwamna shawara kan harkokin tsaro na jihar, suna kan hanyarsu ta zuwa yankin don gudanar da bincike na gani da ido. Ta ce rundunar za ta fitar da cikakken bayani bayan ta samu ƙarin sahihan bayanai.
Wannan hari na baya-bayan nan yana zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun yi wa ayarin masu tafiya jana’iza kwanto a kan hanyar Ochadamu zuwa Ejule a ƙaramar hukumar Ofu ranar 9 ga watan Yuli. A harin, an sace mutane tara, ciki har da jami’ai biyu na hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC), waɗanda ke rakiyar gawar tsohon Mataimakin Kwamandan Hukumar (Deputy Corps Commander), Augustine Ikwue, zuwa mahaifarsa da ke jihar Benue.
PREMIUM TIMES ta rawaito cewa masu garkuwar sun jefar da gawar Mista Ikwue a kusa da Ejule yayin da suka buƙaci kuɗin fansa har Naira miliyan 450 don sakin mutanen da suka sace.
‘Yan sanda sun bayyana cewa jami’an tsaro, da suka haɗa da sojoji, ‘yan banga, da mafarauta na gida, sun ƙaddamar da aikin ceto bayan aukuwar hararin.
Haka kuma, sace ɗaliban na zuwa ne duk da ƙoƙarin da jihohin Kogi da Benue suke yi na ƙarfafa tsaro a kan iyakokinsu. A makon da ya gabata ne jihohin biyu suka ƙaddamar da shirin sintiri na haɗin gwiwa mai suna Operation Handshake Patrol, da nufin inganta musayar bayanan sirri, tarwatsa maboyar miyagu, da bai wa jami’an tsaro damar bin sahun masu laifi ko da sun tsallaka iyakar jihar.