Manchester United ta bayyana sha’awar sayan Gabriel Martinelli, dan wasan gaba na Brazil da Arsenal.

Kafar Calciomercato ta ruwaito cewa wasu manyan ƙungiyoyin Turai suma sun nuna sha’awar daukar dan wasan.

United ta kammala kakar bara da kyau a matsayi na 3, kuma ta bai wa Michael Carrick mukamin koci na dindin a kokarin inganta ƙungiyar a wannan bazara.

Tuni dai United ta riga ta sayi Andrey Santos da Youri Tielemans domin kara wa tsakiyarta karfi.

A cewar rahoton Calciomercato, United na daga cikin ƙungiyoyin da su ka nuna sha’awar ɗan Brazil ɗin, wanda ake ganin yana kan hanyar barin filin wasa na Emirates.

An yi hasashen farashinsa zai kai kusan Yuro miliyan 50 (fam miliyan 42.6).

Wannan ya jawo sha’awar ba kawai United ba, har da Newcastle da Bayern Munich da wasu ƙungiyoyi daga Turkiyya da Saudi Arabia na son sayen Martinelli.

Ana kuma sa ran Arsenal za ta iya rage farashin dan wasan don a yi kasuwar shi a wannan bazara.

Sai dai matsalar da ƙungiyoyin Italiya za su iya fuskanta ita ce a cikin kwantaragin sa ya na karɓar albashin Yuro miliyan 7.5 a shekara, (Fam miliyan 6.4), yayin da yake daukar Fam dubu 180 duk mako.

Juventus na da ‘yan wasa biyu da ke karɓar irin wannan albashi. ‘Yan wasan su ne: Kenan Yildiz da Jonathan David. Roma kuma ba su da wani da ke karɓar haka.

Saboda haka ana ganin zai yi wa ƙungiyoyin Italiya wuya su sa hannu a kan sa da irin wannan kwangila.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *